Saturday, July 5, 2008

SHIN KE MACE ME KOKARI NE?

Abune dayake sananne cewa kina fuskantar matsaloli cikin ranki da kuma zamantakewa a wajen kulla Alaka da aikace - aikacenki, to abinda yakamata kisani shine rayuwa bata rabuwa da wadannan matsalolin, kuma babu shakka nasan cewa sau dayawa kin yi tunani akan wata matsala da ta faru dake, bayan kin dauka mataki domin kiga shin kinyi dai dai koko shin kin yi kuskure? akan matakin dakika dauka, daganan kina kara samun kwarewa wajen magance matsalolinki, ba’a baukatan koda yaushe kizama me ran karfe wajen war - ware matsaloli, amma ga wasu abubuwa dazasu temaka maki wajen hakan

  1. Kiyi abinda ake kira jeranta abubuwa gwargwadon muhimmancin su wato (First thing First) kuma ki tsara ayyukanki,, hakan ze kareki daga damuwa, saboda kina zartar da abinda yakeda muhimmanci sosai, kuma ze rage maki damuwa, saboda ayyukan da bakiyi su ba, basu da muhimmanci sosai.
  2. Kada ki dora ma kanki abinda yafi karfinki, Allah Madaukakin Sarki yace: (La yukallifullahu nafsan illa wus aha Suratul Bakara 286. Ma'ana Allah baya kallafa ma rai face abinda take iyawa. To ya tausaya mana saboda haka yakamata mu tausaya ma kawunanmu, amma batare da kasala ba ko rashin yin aiki, kuma kada kice se kinyi komai da kikeso, wato ki cika komai, domin cika na Allah ne kadai, takenki yazama “Adai daita sahu”
  3. Kada ki shagaltu da aiki fiye da daya, a lokaci guda domin ze kasa hankalinki biyu da kokarin dakikeyi, daga nan baza ki iya yin aiki kwakkwara ba me aminci, abinda yakamata shine: ki kammala wani sannan ki fara nagaba dashi, domin hakan ze saki jin dadi da jin cewa kina samun nasara a rayuwa, kuma ze sa kiyi kwadayin aiwatar da wani aikin.
  4. Wajen alakar ki da sauran jama’a kuma: kiyi kokari ki fuskance su da rashin yin karya kuma bada barin gaskiya ba, A’a cikin natsuwa da hankali, kuma kada kiyi fushi, idan wasu basuyi kawance dake ba, haka kuma ki karbi kuskure idan anyi maki gyara, sawa’un daga kawayenki ne ko wasu daban, ki dauki hakan a matsayin jarrabawa na fadada kirjin ki (wato koyan yin hakuri).
  5. kada kibar jarabawa da baki samu nasara ba akanta, ta hana ki aiwatar da wani aiki, yin tunani akan abinda baki samu nasara ba akansa zesa kiyi wanda yafishi kyau, abinda ya kamata ki dauki rashin samun nasaranki a matsayin ma’auni na samun darasi da kwarewa. Ba matsayin tsoro ba.
  6. Wajen alakanki da sauran jama’a, ki dinga kokarin yawan mur mushi, kuma ki tuna da hadisin da ke cewa “ Yin mur mushin ka ga dan uwanka SADAKA ne" – (wato akwai lada a cikinsa) kuma ki sani dariya na kara maki soyayya dake sa zuciya ta natsu, kuma kiyi kokarin yin Magana da sauti dan kadan domin daga sauti na kara rashin jituwa.
  7. Likitoci suna cewa: Cakuda jiki yana temakawa wajen rage rashin natsuwa da damuwa, To saboda haka ki kwatanta kigani, musamman wajen wanka, da lokacin alwala ki dinga caccakuda yatsun hannu da na kafa.
  8. Ki yi kokari ki dinga yin Zikirin Safiya da na Marece, ze saki a koda yaushe kizama kina tareda Allah, kuma ze kara maki jin cewa Allah yana ganinki a koda yaushe, kuma kina cikin Kariyarsa, kuma kina da ikon ketare kowani abu dayake da wahala, da war - ware matsaloli da datarwansa (ikonsa), ki rokeshi dacewa, da yin dai - dai, Shi Allah yana yaye bakin ciki, kuma yana amsan rokon wanda ya kirasa (mabukaci).
  9. Kada ayyuka ko damuwa susa ki dinga jinkirta sallah, SALLAH hutu ce ga rai kuma natsuwa ce ga zuciya, Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana cewa “Bilal ka hutar damu da Sallah” lokacin da zece ya tada ikama.
  10. Kada kiyi kokarin Boye rashin jin dadinki da damuwanki, A’a kiyarda cewa kinada damuwa, amma ki amince cewa kina da ikon da zakiyi nasara akansa, kuma idan kikaji cewa kinaso kiyi kuka, to kada kiyi kokwanto kiyi kuka da hawaye domin yin kuka ba dalili ne na rashin iko ba ko shi ke nuna kina da rauni, a’a kuka hanya ne na rage damuwa da rai ke ciki.

No comments: